Labarai

Messi Ya Yanke Shawarar Barin Barcelona

Lionel messi

Zakaran kwallon kafar duniya Lionel Messi ya ce zai bar Barcelona, bayan share kimanin shekarar 20 yana taka leda a kungiyar.

 

Kungiyar ta tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na AP a ranar Talata cewa dan wasan Argentinan ya aika mata da wani bayani a rubuce dake bayyana yunkurinsa na barin kungiyar.

 

Wannan sanarwar na zuwa ne kwana 11 bayan ragargazar da Munich ta yi wa Barcelona da ci 8-2 a wasan daf da kusa da na karshe a gasar zakarun Turai, wanda wannan daya ne daga cikin wulakancin kwallon da dan wasan ya gani a tarihin rayuwarsa.

 

Messi wanda ya lashe kyautar Ballon d’O har sau shida ya fara takawa Barce leda ne a 2004, kuma ya lashe gasar zakarun Turai har sau hudu.

@BBCHausa

Back to top button
error: Content is protected !!