Mece Ce Gudunmuwar Kashim Shettima Ga Nasarar Ajandar Sabunta-Fata ?
Shekara Guda A Mulkin Tinubu: Mece Ce Gudunmuwar Kashim Shettima Ga Nasarar Ajandar Sabunta-Fata ?
DAGA: Stanley Nkwocha.
Tun bayan rantsar da su a shekarar 2023, shugaban ƙasa Tinubu da mataimakinsa Kasheem Shettima suna aiki tare kafaɗa da kafaɗa a ƙoƙarin da suke na cika ƙudirori 8 da suke son cimmawa ƙarƙashin shirin “sabunta fata”.
Ba kamar yadda ƴan adawa ke yamiɗiɗin cewa shugaban ƙasa ba ya ba wa mataimakin nasa dama ba. Cewar Stanley Nkwocha, babban mataimaki na musammanga shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, (Ofishin mataimakin shugaban kasa).
Mista Stanley ya kawo wasu daga cikin ayyuka da nasaraorin da shugaban ƙasa ya cimma tare da mataimakinsa kamar haka:
1. Hulɗar Diplomasiyya:
Duk taron da suka halarta a Duniya cikin wannan shekara ɗaya sai sun jawo hankalin masu zuba jari na Duniya a kan su shigo kasuwannin Najeriya su zuba jari. Misali, a watan Nuwamban shekarar da ta gabata ne mataimakin shugaban k`asa Shettima ya bi sahun shugabannin ƙasashen Duniya kimanin 130 a wajen taron BRI karo na 3 da aka yi a kasar Sin, inda ya ja hankalin masu zuba jari daga ƙasashen waje kan samun saukin harkokin kasuwanci a Najeriya.
2. Zaman majalissar tattalin arziƙi (NEC)
A gida Najeriya ma ba a bar Sanata Shettima a baya ba, domin a matsayinsa na shugaban kwamitin tattalin arzikin ƙsa ta (NEC), an samar da sabbin shirye-shirye da ayyuka da dama na gwamnatin tarayya a ƙarƙashin ofishin mataimakin shugaban kasar. Misalai, NEC ta amince da aiwatar da shirin zuba jari na dala miliyan 617.7 a jihohi 36 da babban birnin tarayya kan fasahar sadarwa ta zamani da ƙirƙirarrun hanyoyin saye da sayarwa wato (i-DICE) domin samar da ayyukan yi a bangaren kere-kere da fasaha ta hanyar horas da matasa sama da miliyan 1.2 kai-tsaye kan fasahar ICT da ma wasu aiyukan da ba na kai-tsaye ba da suka kai milyan 5.6 a fadin kasar.
3. Shirin Fulako
Gwamnatin Tinubu ta ƙirƙiro da shirin domin magance musabbabin matsalolin da suka addabi yankunan Arewa wanda suka haɗa da rikici tsakanin manoma da makiyaya, da ‘yan tada ƙayar baya, da ƴan fashin daji da tsabar fatara. A ƙarƙashin wannan shiri za a gina sama da gidaje 1,000 da asibitoci da shaguna a kowace Jaha daga Jihohin Arewa maso Yamma domin biyan diyya ga wanda rikicin ya rutsa da su
4. Shirin Haskaka Nàjeriya.
A watan Fabrairun wannan shekara, mataimakin shugaban Ƙasa Shettima ya ƙaddamar da shirin Light Up South East Initiative, don hanzarta samar da wutar lantarki ga rukunin masana’antu a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.
5. Shirin Bunƙasa Ilimi:
A watan Mayun bana ma, mataimakin shugaban ƙasar ya je Jhar Bauchi inda ya ƙaddamar da shiri mai dogon zango na bunƙasa manyan makarantun gaba da sakandare (ASSEP).
6. Shirin Sake Tsugunar Da Wadanda Rikici Ya ƊaiƊaita:
A ranar Litinin din da ta gabata ne mataimakin shugaban ƙasa Shettima ya ƙaddamar da wani shirin kan yadda Jihohi za su samar da hanyar magance matsalolin muhalli ga waɗanda rikici ya raba da garuruwans.
7. Bunƙasa Ƙananan Sana’o’i:
Shugaba Tinubu ya fara aikin kafa sana’o’i miliyan ɗaya a faɗin Najeriya. A bisa haka ne mataimakin shugaban ƙasa Shettima ya ƙaddamar da dandalin haɓaka ƙananan masana’antun MSME na ƙasa a garin Makurɗi a Jihar Benuwe.
8. Magance Talauci Ta Hanyar Samar Da Kuɗaɗen Shiga:
A cigaba da ƙokarin da gwamnatin Tinubu ke yi na fitar da ‘yan Najeriya daga ƙangin talauci, mataimakin shugaban ƙasa Shettima, a ranar 25 ga watan Afrelun bana, ya ƙaaddamar da shirin gwamnatin tarayya na Aso Accord on Economic and Financial Inclusion. Wani shiri mai bangarori da dama da aka tsara domin samun damar shiga tsare-tsaren samun kuɗaɗen shiga a faɗin Najeriya.
9. Gina Ƙasa Ta Hanyar Abinci Mai Gina Jiki:
A ƙarƙashin ƙudirin gwamnatin Tinubu na samar da abinci mai gina jiki da rahusa, kwanan nan mataimakin shugaban ƙasa Shettima ya ƙaddamar da wani gagarumin shiri na inganta abinci mai gina jiki a fadin Najeriya.
10. Ba Sani Ba Sabo Kan Noma:
Bisa la’akari da ɓarnar da aka tafka a wasu muhimman ɓangarori da suka haɗa da noma na tsawon shekaru. Da hawa karagar mulki Shugaba Tinubu a shekarar da ta gabata, ya fara aiwatar da sauye-sauye masu tsauri don kawo gyara a fannin noma. Shugaban ya bayyana wasu tsare-tsare da suka hada da faɗaɗaa filayen noma zuwa hekta 500,000, da samar da rancen kuɗaɗe masu ƙarancin ruwa ga manoma da zuba jari a fannin noman rani.
A Shekarar bana, mataimakin shugaban ƙasar ya fitar da nasa tsarin ƙarfafa manoman ƙasar nan don cimma nasarar shirin samar da abinci da aikin noma na gwamnatin Tinubu. Shirin mai suna Kashim-Shettima Foundation’s Agricultural Empowerment Programme, wanda aka ƙaddamar da shi a Jihar Kaduna, ya nuna cewa an fara rabon taraktoci, da iri, da takin zamani, da magungunan kashe kwari, da sauran muhimman kayan noma ga manoman da za su amfana da noman shekarar 2024.