Labarai

Me Ke Shirin Faruwa Tsakanin Sarkin Katsina Da Gwamnan Jihar

Me Ke Shirin Faruwa Tsakanin Sarkin Katsina Da Gwamnan Jihar Dikko Raɗɗa

Rahotanni na nuni da cewa a jiya asabar ne aka wayi gari da ganin wata takarda da Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya aike wa da Sarkin Katsina yana neman ƙarin bayani daga Sarkin.

Katsina

Leadership ta ruwaito cewa An dai tura wannan takarda ne zuwa ga masarauta daga ofishin sakataren gwamnatin jihar Katsina inda ake neman Sarkin Katsina Alhaji abdulmumini Kabir Usman da ya yi ƙarin bayani akan rashin hawan wasu Hakimai a Babbar Sallah.

Takardar mai neman karin bayani kan wata takarda da aka aike a ranar 7 ga watan Yuni 2024 da lamba S/SGKT/77/S 2/T tana neman Sarki da ya yi bayanin me ya sa wasu hakamai na masarautar Katsina ba su yi hawan sallah ba kamar yadda gwamnati ta bada umarni.

Daman dai ana ta yaɗa jita-jitar cewa dangantaka ta fara tsami tstsakani Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa da masarautar Katsina zargin da yanzu ke neman zama gaskiya.

Domin a baya an riƙa yaɗa labarin cewa gwamnatin jihar ta tsaida dakatar da Magajin garin Katsina wanda babban ɗa ne ga Sarkin Katsina, amma dai babu wata takarda da ta nuna hakan a gwamnatance.

Wata majiya ta ce tuni Gwamnan Katsina ya shirya kirkira wasu sabbin Hakimai a karkashin masarautar.

Shin ko me yake shirin faruwa a wannan masarauta mai daɗaɗɗen tarihi, Allah shi ne masani, tambayar da mafi yawan jama’a ke yi ke nan a halin yanzu.

Yanzu dai jama’a da dama na sauraran irin amsar da masarautar za ta maida wa Gwamnatin Jihar Katsina a kan wannan batu da ya taso.

Idan za a iya tunawa a lokacin bikin hawan Sallah ƙarama, Gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya gargadin cewa daga yanzu dole ne Kowane hakaimi ya yi hawan Sallah sai dai mai lalurar tsufa ko rashin lafiya ko kuma tafiya Makka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!