Mazaunai na ne; ƙara girma su ka yi; Babu ciko – inji Rahama Sadau
Fitacciyar jarumar Kannywood
, Rahama Sadau ta bayyana cewa mazaunanta da a yanzu suka kara auki fa ba na roba bane ko kuma ciko; na gaske ne.
Jarumar ta faɗi haka ne a amsar da ta ba mujallar Fim lokacin da ta tambaye ta idan na roba ne kamar yadda wasu ke tunani, musamman bayan sun ga wani hoto na jarumar inda ta juyo baya kamar ta na nuna wa mutane irin abin da ta mallaka.
Hoton ya haifar da muhawara a tsakanin ‘yan kallo; yayin da wasu ke cewa mazaunan Rahama ciko ne aka yi, wasu kuma na cewa a’a, na gaske ne.
Sanin kowa ne cewa wasu matan kan ɗaura na roba don su ƙara wa kan su diri, kamar yadda wasu matan ke ƙara gashin kai ko ƙirji.
Da Turanci, jarumar ta ce, “REAL! By the way it’s called GROWTH. Sai hamdala!” Wato ita abin ta na gaske ne, kuma ƙara girma su ka yi, don haka ta na godiya ga Allah a kan hakan.
A kan ko wani zai zage ta kan wannan lamari, Rahama ta ce ita ba ta damu ba, domin “zagi ai ba ya fitowa a jiki.”
Ta ce duk wanda zai zage ta ai sai ya je yai ta yi. “Ai kowa da ra’ayin sa. Ni hanyar da na zaɓa kenan.”