Labarai

Matashi Mai Satar Fitilu a Gadar Babangida a Legas Ya Shiga Hannu

Mubarak Abdullahi Matashi Mai Satar Fitilu a Gadar Babangida a Legas Ya Shiga Hannu

Jami’an tsaro na Legas Rapid Response Squad (RRS) da misalin karfe 10:00 na safe a ranar Juma’a sun kama wani da ake zargin dan fashi ne a lokacin da ya ke cire fitilar f titi na LED a sabuwar gadar Third Mainland Bridge da aka gyara, fadar da aka fi sani da gadar Babangida

Wanda ake zargin, mai suna Mubarak Abdullahi mai shekaru 18 da ke zaune a unguwar Makoko, a lokacin da aka kama shi, ya cire 10 daga cikin fitulun titin LED da aka lakaye a kan titin domin kara ganin masu amfani da hanyar.

Jami’an tsaro sun kama wanda ake zargin da hannu wajen sintiri a kan gadar da misalin karfe 10:00 na safiyar yau.

Kwamandan Rundunar Rapid Response Squad (RRS), CSP Yinka Egbeyemi makonnin da suka gabata, ya tura mahaya babura aikin sintiri na tsaro na sa’o’i 24 a yankin domin lura da zirga-zirga da kuma kula da ababen more rayuwa da aka sanya a kan gadar.

Back to top button
error: Content is protected !!