Matasan Arewa Sun Bukaci A Kama Kwankwaso
Matasan Arewa Sun Bukaci A Kama Kwankwaso
Kungiyar Matasan Arewa sun yi kira da a Kama Rabiu Musa Kwankwaso kan kalaman da yayi na tunzura Matasa
A jiya ne Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso Yayi Wani jawabi a mahaifarsa ta Madobi yayin ƙaddamar wata hanya mai tsawon kilomita 82. Inda Yace “akwai wasu mutane ne da suke son suci zarafin mu da sunan siyasa wanda ba zamu lamunci hakan ba ko waye shi, dan haka kuma a shirye muke damu taka duk wanda yake da niyyar taka mu a siyasar jihar kano” inji kwankwaso.
Kungiyar Matasan Arewa A ƙarƙashin Jagorancin Shugaban ta Comr Ambasada Abdul Danbature Ta bayyana takaicin ta kan kalaman tsohon Gwamnan Rabiu Musa Kwankwaso. Inda Ta bayyana cewa a matsayin sa na ɗaya Daga cikin Jigajigan siyasar Arewa bai kamata yana furta ire-iren waɗannan kalaman ba da zasu janyo hatsaniya da Rasa rayukan dubban al’umma ba.
Ƙungiyar ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Yan Sanda DSS da sauransu dasu gaggauta cafke Rabi’u Musa Kwankwaso Tare da tilasta shi ya janye kalamansa na haifar da Fitina a jihar Kano wanda ta kasance cibiyar kasuwancin Arewacin Najeriya
A ƙarshe Ƙungiyar Ta gargadi yan siyasar Arewacin Najeriya dasu guje furta kalamai da zasu janyo hatsaniya da tashin hankali a arewacin Najeriya. Musamman a dai-dai lokacin da Matasan arewacin Najeriya suka kauracewa bangar Siyasa Bazamu amince da duk Wani mutum da zai dawo da bangar siyasa ba kowanene shi inji kungiyar
Daga Comr Ambassador Abdul Hameed Danbature Shugaban Ƙungiyar Arewa Youth Assembly for Good Leadership