Matanen Kano Ku Shirya Murnar Samun Nasarar Gawuna
Rarara ya yi kira ga Al’ummar Jihar Kano da su yi murnar Nasarar Gawuna cikin natsuwa
Fitaccen mawakin Siyasa a nahiyar Afrika, Dauda Kahutu Rarara ya yi kira ga Al’ummar Jihar Kano, da za su fito murna a lokacin da za a bayyana nasarar karshe ta Gawuna/Garo da su fito cikin natsuwa ba tare da tada hankalin kowa ba.
A cewarsa, babu abin da su ke so irin ci gaban Jihar Kano, don haka za su fito murna bayan yanke hukuncin karshe, amma ba za su fito don tada hankalin kowa ba, ko kuma don kona dukiyar kowa ba, ko yin wata hayaniya da za ta sanya Al’umma dar-dar ba.
Rarara ya bayyana haka ne a wani gaggarumin taro da ya shirya a Ranar Litinin, 11 ga watan Disamba 2023 dakin taro na Otal din Bristol da ke Kano.
Sannan ya yi wa masoyansa albishir da sabuwar wakar sa da zai saki mai taken 4-0.
Sako Daga Abdullahi Al-Hikima







