Kannywood
Matan Da Zan Iya Aura A KannyWood Idan Na Sami Dama
Da Za’a Ba Ni Za6in Matar Aure A Masana’antar KannyWood Da Na Aure: Hadiza Gabon, Aisha Humaira, Da Uummi Karama, Cewar Yusuf Sasen Lukman Labarina.
Fitaccen matashin ɗan wasan Hausa, mai suna Lukman a cikin shirin “Labarina” ya bayyana cewa da ace za a ba shi zaɓin ya auri mata a Kannywood to da ya auri mata uku ya rufe ƙofa matasan su zama huɗu cif! Cif!! ƙari akan matar da ya ke da ita kenan.
Lukman ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa da Dokin Ƙarfe TV ta yi da shi a yau inda ya bayyana kamar haka:
“Da ace za a ba ni zaɓi na auri mata a masana’antar Kannywood to da na auri tsala-tsalan ƴan mata su: Hadiza Gabon da A’isha Humaira, da Ummi Ƙarama na cike mata huɗu Cif”. Cewar Lukman na cikin shirin Labarina.







