Kannywood

Matan Da Suke Son Aurena Sun Fi Dubu: Dantani Mai Shayi

Tauraron fina-finan Hausa Murtala Alasan wanda yake fitowa a shirin Dadin Kowa na tashar Arewa24 a matsayin Dan Tani Mai Shayi ya bayyana cewa yana da masoya da yawa.

Ya bayyana hakane a wata hira da Mujallar Fim ta yi dashi.

Mujallar ta tambayeshi shin ya yake yi kasancewar yana da masoya da yawa idan ya hadu da Mutane?

Kuma wannan tambayar da ka yi mini ta cewar ina shayi, haka mutane su ke yi mini a duk inda na je, kuma a yanayi irin namu babu irin jama’ar da ba ma haɗuwa da su: zaurawan ne ‘yanmatan ne, wanda kuma a nan mu na samun ƙalubale wanda dole mu ke yin taka-tsantsan da kuma bi a hankali; kowa ya ce ya na son ka! To mace sama da dubu kowacce ta ce ta na so ta aure ka, yaya za ka yi da su? Ka ga dole sai ana yin taka-tsantsan! Kuma su matan ya kamata dai su rinƙa yi mana uziri.

Back to top button
error: Content is protected !!