Labarai
Yan Matan Arewa ma sun Fara Auren Turawa
Shin Da Gaske Ne Ya Tabbata Yan Matan Arewa ma sun Fara Auren Turawa? Idan Har Da Gaske Ne, Kenan Zamu Iya Cewa Sun Fara Ramawa, Fanin Cewa Samarin Arewa Su Suka Fara Auro Matan Turawa.
A yayin da ake tsaka da muhawara kan soyayyar da wani matashi dan Panshekara yake yi da wata baturiya inda wasu suka yabeshi wasu kuma suka rika fadin akasin haka. Wasu hotunan wata matashiya da bature suma sun bayyana.
Hotunan da babu sahihanci akan labarin dake tattare dasu na ta yawo a shafukan sasa zumunta inda wasu ke lakabin cewa Mata ma sun fara ramuwa akan auren turawa da matasan Arewa suka fara yi.