Kannywood

Yakamata Mata Su Dinga Bincike Kafin Su Yi Aure -Rukayya Dawayya

Fitacciyar jarumar masana’antar Kannywood a Najeriya, Rukayya Umar Santa, wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya, ta shawarci mata da ke shirin yin aure da su rika yin bincike kafin su tsunduma cikin harkar ta aure.

Jarumar wacce ta samo sunan “Dawayya” daga wani fitaccen fim dinta “Dawayya,” ta ce a lokuta da dama, matan da suka dade ba su samu miji ba, kan yi aure ba tare da sun gudanar da kwakkwaran bincike ba.


Dawayya ta tana magana ne kan sabon fim dinta mai suna “Ummi Sambo” da aka haska a farkon watan Disambar nan, yayin wata hira da ta yi da wakiliyar Muryar Amurka Baraka Bashir.


“Matsalolin da suka fi damun mu, su ne ta yawan mutuwar aure da kuma yin aure babu bincike.” Ta ce, a lokacin da aka tambaye ta jigon labarin fim din na “Ummi Sambo.”
Ta kuma kara da cewa, “muna da manyan ‘yan mata da suka dade ba su yi aure ba, wasu sa’aninsu ma sun kusa aurar da ‘ya’ya, to wannan abin yana sa kowa ya zo miki sai ki yi aure.”


“Wannan ita matsalar da ke damun mu, shi ya sa muka dauki wannan bangare, a matsayina na mace.” Dandalin VOA

Back to top button
error: Content is protected !!