Labarai
Masu Murna Da Cin Fuskar Da Aka Yi Wa Danbilki Kwamanda Sun Ji Kunya
Masu Murna Da Cin Fuskar Da Aka Yi Wa Danbilki Kwamanda Sun Ji Kunya, Cewar Barista Abba Hikima
Shahararen Lauyan nan na Kano, Barista Abba Hikima ya ce abun kunya ne a samu ɗan adam yana murna da cin zarafin ɗan adam ko da kuwa da bambancin addinni ne, balle siyasa.
“Idan Danbilki Kwamanda laifi yayi, sai a hukunta shi, amma cin zarafi irin wannan abun Allah-wadai ne”. Inji Abba Hikima.