Labarai

Masha Allah : Sunan Muhammadu Na Daga Cikin Sunaye Goma (10) Da Aka Fi Radawa Sabbin Yaran Da Aka Haifa A Kasar Amurka

MUSULUNCI A KASASHEN TURAI DA AMURKASunan Muhammadu Na Daga Cikin Sunaye Goma Da Aka Fi Radawa Sabbin Yaran Da Aka Haifa A Kasar AmurkaDaga Ash-sheikh Ahmad Muhammad Gombe mazaunin Kasar Amurka

A jiya Jumu’a Dec 6, 2019 da misalin karfe 12:22pm agogon gabashin Amurka (EST) gidan talabijin na CNN ya bada labarin cewa: binciken hukumar dake tattara sunayen yaran da aka haifa a wannan shekara yanuna cewar sunan Muhammad da Ãliya suna daga cikin sunaye goma daga akafi sanyawa yaran da aka haifa a wannan shekarar ta 2019.

Lallai hakan yana nuna karuwar musulmai da kuma cigaba da musulunci ke kara samu a wannan kasa, Allãhu Akbar!.Dama dai masana sunyi hasashen cewa nan da wasu shekaru masu zuwa musulunci zai rinjayi sauran addinai a manyan kasashen Turai da Amurka.

Ko shakka babu cigaban musulunci a wadannan kasashe cigabane kuma daukakar addinine.Kamar yadda addini ya kara daukaka a lokacin da yaci Daular Farisa da Rum a lokacin Sahabbai haka zai ci wadannan kasashe in shaa Allah.

Ko shakka babu ga duk mutumin da yake zaune anan Amurka ko kuma wata kasa daga cikin manyan kasashen Turai indai yana harkaraddini bakawai yana holewar sa ba toh yana ganin alamun haka da yardar Allah.Yaa Allah Ka tabbatar da mu akan addinin Ka har zuwa karshen rayuwar mu!

Back to top button
error: Content is protected !!