Kannywood

Maryam Booth Ta Nemi Dezell Ya Biyata Diyyar 300M A Kotu

Sananniyar jarumar fina-fina Hausa, Maryam Booth, ta maka tsohon saurayinta, Ibrahim Ahmed Rufai a gaban kotu sakamakon zarginsa da ta ke da yada bidiyon tsiraicinta ba tare da izininta ba.

Idan za mu tuna, makonni kadan da suka gaba ne kafafen sada zumuntar zamani suka hautsine da bidiyon tsiraicin jarumar. Lamarin da ya jawo martani da cece-kuce daga jama’a masu tarin yawa.

Bayan kwanaki kadan da walllafa wannan bidiyon, jarumar ta fito ta bayyana wanda ta ke zargi da wannan aika-aikar. Ta ce tsohon saurayinta kuma matashin mawaki Deezell ne da wannan aika-aikar. A don haka ne kuwa jarumar ta sha alwashin daukar matakin shari’a a kan tsohon saurayin nata da ya ci amanarta.

A karar da ta shiga a ranar 27 ga watan Fabrairun 2020 a gaban wata babbar kotun tarayya da ke birnin tarayyar Abuja, Booth ta yi ikirarin cewa tsohon saurayin nata ya dauka wannan bidiyon ne ba tare da izininta ba a ranar 27 ga watan Fabrairun 2017 a dakin otal din Nanet Suit da ke Abuja.

A don haka ne kamar yadda ta ce, wanda take karar ya fara yi mata barazanar sakin bidiyon tsiraicin na ta tare da bukatar wasu kudi daga hannunta. Ya ce zai wallafa bidiyon matukar ba ta bashi kudin ba.

Ta kara da cewa, a lokacin da ba ta ba shi kudin ba, sai ya gangara tuwita da sauran kafafen sada zumuntar zamani ya wallafa bidiyon.

A don haka ne Booth ke bukatar kotun da ta umarci Rufai da ya dakata da ci gaba da yada bidiyon a tuwita da sauran kafafen sada zumuntar zamanin.

Jarumar ta kara da rokon kotun cewa ta tuhumi Rufai da laifin nadar bidiyon ba tare da izininta ba da kuma bata mata suna.

Ta kara da rokar kotun da ta tirsasa Rufai a kan ya biya ta kudi har naira miliyan 300 na bata mata suna da ya yi.

Back to top button
error: Content is protected !!