Kannywood

Maryam Booth Ta Bayya Wanda Fitar Da Bidiyon Tsaraicinta

Jaruma Maryam Abdullahi, Da Akafi Sani Da Maryam Booth, Ta Fito Tayi Magana Tun Bayan Fitar Da Bidiyon Tsaraicinta Da Akayi A Ranar 6/02/2020.

Jarumar Dai Taja Baya Tayi Shiru Game Da Lamarin, Sai Dai Daga Baya Ranar 08/02/2020 Da Misalin Karfe 8 Da Wasu Mintoci, Ta Fito Tayi Bayani. A Shafin Twitter.

Inda Take Cewa Kwatsam Taga Wani Guntun Bidiyo Na Yawo A Shafin Sada Zumunta, To Tayi Shiru Ne Kawai Domin Taga Yanda Jami’an Tsaro Zasuyi Da Lamarin.

Ta Kara Da Cewa Ita Ta Tabbatar Da Cewa Ibrahim Ahmad Rufai Wanda Akafi Sani Da Dezell, Shine Mutumin Da Take Zarginsa Da Yada Wannan Guntun Videon, Tace Bazata Canja Maganarta Ba, Akan Cewa Shine Ya Wallafa Bidiyon Nata Yayin Da Take Kokarin Canja Kaya.

Ta Kuma Ce Tun Bayan Dasu Rabu Dashi A Matsayin Saurayi Da Budurwa, Yata Barazanar Sakin Bidiyon Nata, Kuma Yasha Tambayarta Kudi Akan Idan Bata Bashi Ba, Zai Iya Sakan Videon.

Tayi Shiru Ne Kawai Saboda Tana Matsayin Wata Jaruma Mai Mabiya Da Dama A Ciki Da Wajen Nigeria. Kuma Ana Ganin Kima Da Martabarta.

Tace Jami’ai Sunanan Suna Yin Duk Mai Yiwuwa Don Ganin An Kwato Mata Hakkin Sunan Daya Bata Mata.

Daga Karshe Tama Yan Uwanta Da Abokanta Da Kuma Masoyanta Da Haryanzun Suke Tare Da Ita Kuma Suke Nuna Mata Kauna.

Back to top button
error: Content is protected !!