Maryam Babban Yaro Tayi Sabon Aure
MashaAllah! Itama Jaruma Maryam Babban Yaro Daya Daga Cikin Zawarawan KannyWood Ta Shiga Daga Ciki, Ranar Asabar 17 Ga Watan 12 Ne Aka Daura Auren Tsohuwar Jarumar Ta KannyWood Yar Garin Jos Maryam Jibril Gidado, Wacce Akafi Sani Da Maryam Babban Yaro.
Jarumar Dai Tana Daya Daga Cikin Jarumai Wanda Suja Zarensu A Shekarun Baya, Inda Fim Din Mai Suna Babban Yaro, Na Adam A Zango, Wanda Ayi Shi A Shekarar 2012. Shine Fim Din Da Ya Fito Da Jarumar.
Sai Dai Kuma Daga Baya Ne Harkar Na Fim Yazo Ya Qarewa Jarumar, Bayan Da Kwata Kwata A Daina Ganin Giftawarta A Kowane Fim, Hakan Yasa Jarumar Tayi Sanyi.
Idan Baku Manta Ba A Kwanakin Baya Ne Aka Samu Cece Kuce Inda Mutane Su Taso Jarumar A Gaba, Kan Cewa Ta Qare Mata. Inda Jarumar Ta Fito Ta Kare Kanta,
Ana Cikin Haka Kuma Sai Ga Katin Gayyatar Aurenta Inda Mu Sami Katin Gayyatar Auren Ta Shafin Abokiyar Sana’arta Jamila Nagudu, Kamar Yanda Yazo A Jikin Katin Gayyatar, Jarumar Ta Angonce Ne Da Wani Mutum Mai Suna Alhaji Abdulmumin Hassan, Inda Aka Daura Auren Ranar Asabar Da Misalin Karfe Sha Daya Na Safe, A Unguwar Gangare Dake Cikin Garin Jos.
Allah Ya Basu Zaman Lafiya Amin