Kannywood

Manyan Rikice-Rikice Guda 5 Da Su Faru A Kannywood a 2019

Furodusoshi sun bayyana cewa ba a siyan fina-finai a wannan shekarar saboda nuna shi da ake kadai a sinima. Hakazalika anyi fadace-fadace tsakanin ‘yan wasa wanda hakan ya jawo tashin-tashina kala-kala a masana’antar.

Ga manyan al’amuran masana’antar da suka jawo cece-kuce a 2019.

1. Ali Nuhu ya maka Adam Zango a kotu

Anyi wannan fadan ne a watan Afirilu. Ali Nuhu ya maka Adam Zango a kotu sakamakon zarginsa da yake da bata masa suna.

A wani bidiyon da Adam ya fitar, ya zargi Ali Nuhu da goyon bayan magoya bayansa don sun zagi mahaifiyarsa. Da farko Nuhu bai mayar da martani ba amma daga baya ya kaishi kara. Sa hannun manyan masana’antar ne yasa ya janye karar.

2. Deeni da Zeezee sunyi fada saboda wani kudi da Atiku ya bada

Jaruman biyu sunyi kaca-kaca ne sakamakon zargin juna da suka yi a kan rub da ciki a kan wasu kudi da Atiku ya basu.

ZeeZee ta zargi Zahradeen da bata kaso kadan daga ciki. Ta zargi Sani Danja, Zahradeen Sani, Fati Mohammed, Al’amin Buhari da Imrana Mohammed da diban kudin da Atiku ya baiwa masana’antar don amfanin kansu.

Daga baya Deeni ya kaiwa ‘yan sanda kara amma ya janye bayan da aka saka baki.

3. Hadiza Gabon da Amina Amal

A 2019 din nan ne Hadiza Gabon ta je har gida tayi wa Amal dukan tsiya sakamakon zarginta da tayi da madigo. Bayan haka ta dau bidiyon ta saka a Instagram, lamarin da ya jawo hankulan masu rajin kare hakkin dan Adam.

Daga baya dai an sasanta su amma har yau basu ga maciji.

4. An zargi Zango da diban yara kanana don yi sabbin fina-finansa

Wani malami ya zargi Adam Zango da diban kananan don fitowa a sabbin fina-finansa. Malamin ya zargi Zango da yin amfani da damar wajen sanya yaran su bar karatu don komawa wasan kwaikwayo.

Bayan kwanaki kadan, Zango ya fito tare da rantsuwa da Qur’ani wajen karyata malamin, lamarin da ya jawo cece-kuce.

5. An kalubalanci Rahama Sadau a kan hada shagalin bikin zagayowar ranar haihuwarta.

Da yawa daga cikin ‘yan fim din sun kalubalanci Rahama Sadau a kan shigarta a wajen taron.

Bayan haka, ta bude wajen cin abinci tare da gidan shan Shisha, lamarin da ya jawo cece-kuce daga jama’a da yawa.

Back to top button
error: Content is protected !!