Kannywood

Bleaching Mai tsada muke yi shi yasa mu fi dan uwan haske

Rahama Sadau ta shirya tafiya kuma ta kwashi yan uwanta tare da wallafa hotunansu a kafar sada zumunta ta Instagram

Ta bukaci mabiyanta su cinka inda suka nufa amma sai wani ya tambayeta dalilin da yasa kaninta baki su kuwa farare

A take jarumar ta bayyanawa saurayin cewa man bilicin suke shafawa mai tsada shiyasa suka zama farare tas

Rahama Sadau ta shirya tafiya inda ta kwashi ‘yan uwanta mata gaba dayansu harda dan uwanta Abba Sadau wanda shi kadai ne namiji a cikinsu inda suka yi hoto kuma ta wallafa shi a shafinta na Instagram tare da cewa masoyanta su canki inda suka nufa.

Kowa yayi ta fadar inda suka dosa a nashi zaton wasu kuma suna yi mata fatan alkhairi da yaba yadda take son ‘yan uwanta, amma a ciki sai wani matashi mai suna Gaddafi Ibrahim yayi mata tambayar da ta sa dole ta mayar mishi da martani.

Gaddafi Ibrahim ya rubuta mata cewa, “Rahama Sadau ya aka yi wannan kanin naki yazo a baki kuma duk kun fi shi kyau.”

Rahama Sadau ta bashi amsa da cewa “muna shafa man bilicin mai tsada ne.”

Wannan amsar da ta bada kuwa ta ja hankalin daukacin mabiyanta, inda suka dinga nuna jin dadinsu da irin wannan amsar tata. Sun ce gara da ta bashi amsa dai-dai da tambayar da yayi irin ta shashanci. Wasu kuwa sun nuna wa matashin rashin kyautawarsa da irin wannan katobarar da yayi.

Daga karshe dai Rahama ta sake wallafa hotunansu ita da ‘yan uwan nata bayan sun sauka a Dubai. Kamar yadda tashar tsakar gida ta YouTube ta ruwaito.

Back to top button
error: Content is protected !!