Kannywood

Addu’a Ta Musanman Ga Marigayi Aminu S Bono

Yanda Jaruman KannyWood Su Shirya Addu’a Ta Musanman Ga Tsohon Abokin Aikinsu Marigayi Aminu S. Bono,

Saƙon Godiya Ta Musamman Daga Ƙungiyar Musu Shirya Fina-finai Ta Masana’antar Kannywood

Ƙungiyar diractoci ta kannywood (PROFDA) ta na miƙa saƙon ban-gajiya ga mahalarta taron Addu’ar bakwai da aka yi wa ɗaya daga cikinsu, marigayi Aminu S. Bono wanda ya cika kwanaki 7 da amsa kiran Ubangiji a jiya.

Ƙungiyar ta yi masa Addu’a da sauran ƴan’uwa ƴan masana’antar da suka rasu kan Allah Ubangiji ya ji ƙansu da rahama Ya kyautata namu ƙarshen.

Ƙungiyar ta (PROFDA) tana kuma ƙara godia ga jama’ar da suka bada tallafin don a tallafawa iyalasa. Sanna tana ƙara godiya ga Abdul Amart bisa namijin ƙoƙari da ya yi wajan siyawa iyalan marigayi Aminu S. Bono Gida. Tare da fatan Allah ya saka masa da alkhairi da dukkan waɗanda suka taimaka da kuɗi ko addu’a.

Daga ƙarshe ƙungiyar ta (PROFDA) ta ƙara godiya tare da fatan Allah Ya taimaki Kannywood.

Back to top button
error: Content is protected !!