E News

Makarantu Wajen Neman Ilmi Ne Ba Fagen Satar Mutane Ba

Makarantu Wajen Neman Ilmi Ne Ba Fagen Satar Mutane Ba

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya bayyana haka a wani sakon maraba da nasarar kubutar da Daliban Makarantar Kuriga ta jahar Kaduna da jami’an tsaro suka samu.

Shugaban ya ce dole ne a kula da tsaron lafiyar Makarantu da dalibai, a domin tabbatar da hakan dole ne a sami hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi domin samun ingantaccen sakamako ta fuskar tsaro.

Shugaban ya yaba wa mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu da sauran hukumomin tsaro, da ma gwamnatin jihar Kaduna bisa jajircewar da suka nuna wajen ganin an shawo kan wannan lamarin ba tare da asarar rayuka ba.

Kazalika Shugaban ya yi maraba da sakin daliban makarantar Tsangaya da ke jihar Sokoto, inda ya yaba wa duk bangarorin da suka yi namijin kokari don samin wannan nasara.

Shugaban ya sha alwashin cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen samar da sabbin dabarun da za su tabbatar da cewa makarantunmu sun kasance amintattun wuraren daukar ilmi, maimakon zamowa dakunan sace-sacen mutane.

Chief Ajuri Ngelale Mai bai wa shugaban kasa shawara ta musamman kan kafofin yada larabai da huldar Jama’a) Maris 24, 2024.

Back to top button
error: Content is protected !!