E News

Majasar Dattawan Ta Janye Dakatarwar Datayiwa Sanata Abdul Ningi

Majasar Dattawan Ta Janye Dakatarwar Datayiwa Sanata Abdul Ningi.

Sanata Abdul Ningi wanda Majalisar Dattajai ta Dakatar ranar 12 ga watan Maris bayan kwarmata cewa shugabancin Majalisar sunyi cusen wasu aiyuka acikin kudirin kasafin kudin shekarar 2024 wanda ba’ayi cikakken inda za’a gabatar da aiyukanba.

Majasar Dattawan ta janye dakatarwa datayiwa Sanata Abdul Ningi Dan Jam’iyyar PDP mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya bayan wani zaman sirri na kimanin awa daya da Majalisar yagabatar.

Batun janye dakatarwa yabiyo bayan wani kudiri da Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Sanata Abba Moro yagabatar Ayau Talata, kudirin kuma yasami goyon bayan mataimakin Shugaban marasa rinjaye Olalere Oyewunmi da Bulaliyar marasa rinjaye Osita Ngwu.

Sanata Ningi wanda yayi buncike na kashin kansa akan kundin kasafin kudin shekarar 2024 yagano wasu aiyuka na Biliyoyin Naira da’a saka ba’ayi cikakken bayanin inda za’a gabatar dasuba.

Kuma lokacin da Sanata Ningi yayi wancan kwarmaton shine Shugaban kungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya. Sanata Abba Moro lokacin dayake gabatar da kudirin yace amadadin kingiyar Sanatoci marasa rinjaye sun dauki nauyin dukkan wani laifin da majalisar take tuhumar Sanata Ningi dashi kuma bayar da Hakuri a madadinsa.

Back to top button
error: Content is protected !!