Labarai
Majalisar Tarayyar Najeriya Tayi Watsi Da Yarjejeniyar “SAMOA”
Majalisar Tarayyar Najeriya Tayi Watsi Da Yarjejeniyar “SAMOA”
Bayan da ɗan majalisar wakilai, Aliyu Sani Madaki ya kai ƙudiri a majalisar wakilai na daƙatar da yarjejeniyar “SAMOA” da ake zargi da Auren Ji’nsi.
Majalisar Wakilai ta nemi Gwamnatin tarayya da ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar Samoa bisa zargin Maganar “LGBTK
Majalisar ta umarci kwamitinta mai kula da tsare-tsare na kasa da ya binciki yarjejeniyar cikin makonni hudu.
Kudurin Majalisar ya biyo bayan kudirin da shugaban marasa rinjaye, Aliyu Madaki, da wasu mutane 87 suka Gabatar a zauren majalisar a Yau Talata.