Kannywood
Mahaifiyar Afakallahu (Tsohon Shugaban Hukumar Tace Fina Finai) Ta Rasu
INNA lillahi wa inna ilaihir raji’un! Allah ya yi wa mahaifiyar tsohon Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Isma’ila Na-Abba (Afakallahu), rasuwa.
Hajiya Fatima Mu’azu (Gwaggo) ta rasu ne a yau a garin Kano, ta na da shekaru 97.
Za a yi jana’iza anjima da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, bayan sallar la’asar a gidan sa da ke unguwar Maidile kusa da masallacin Juma’a na Ansar.
Allah ya jiƙan Gwaggo da rahama, ya kuma albarkaci dukkan abin da ta bari.