Kannywood

Mahaifiya ta ce ta karfafamin shiga fim – Raliya Dadin Kowa

Matashiyar jarumar nan Amina Lawan wadda akafi sani da Raliya Dadin Kowa ta bayyana cewa mahaifiyarta ce ta bata kwarin gwiwar shiga fim.

Raliya ta bayyana hakan ne yayin zantawar da tayi da Freedom Radio inda tace “Ina sha’awar na shiga harkar fina-finan Hausa domin nima na bada gudummuwa ta wajen wayar da kai da ilimantar da al’umma, kuma na samu cika burina kasancewar mahaifiya ta tana cikin iyaye a masana’antar, don haka ta karfafamin gwiwa ba tare da wani cikas ba”.

Mahaifiyar jaruma Amina ita ce Hajiya Halima Lawan wadda akafi sani da Sabuwa matar Ayuba mai gadi a shirin Dadin Kowa.

Wannan dai na zuwa ne lokacin da wasu al’umma ke sukar jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa da cewa mafi yawa basu cika amincewa ‘ya’yan su su shigo a dama dasu a masana’antar ba.

Shekaru hudu kenan da matashiyar jarumar Amina Lawan mai shekaru 20 ta fara taka rawa a fina-finan Hausa, inda take Film da kuma waka.

Sai dai Tauraruwar Jarumar ta haska ne bayan fitowar ta a shirin Dadin Kowa wadda take cikin manyan jarumai da jama’a ke tausayawa kasancewar ta fito a cikin wahala.

Back to top button
error: Content is protected !!