Mace Ta Zama Shugabar Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa Ta Kasa
A Karon Farko Mace Ta Zama Shugabar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA)
Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin mace ta farko wato Malama Zubaida Umar a matsayin Darakta-Janar ta Hukumar(NEMA)
Malama Zubaida ita ce mace ta farko da aka nada a matsayin Darakta-Janar ta wannan hukuma mai muhimmanci, kuma nadin nata ya kara jaddada kudirin shugaban kasar na samar da daidaito a bangaren rabon mukamai tsakanin maza da mata.
Sabuwar Darakta-Janar din ta shafe shekaru 20 tana aiki a fannoni daban-daban, kazalika memba ce ta Cibiyar Ma’aikatan Banki na Chartered da Cibiyar Kula da Ba da Lamuni.
Shugaban kasa na sa ran cewa sabuwar Darakta-Janar za ta kawo sauye-sauyen da ake bukata musamman a bangaren kudi da tsarin gudanarwa a hukumar.
Allah Ya taya riko.