Ungategored

Ma’aurata zallah : Hanyoyin Saukewa Miji Gajiya (1)

Gajiya dai wani al’amari ne dake jikin ko wani halitta da jini yake gudana a jikinsa. Don haka duk wani abu mai rai yana iya jin gajiya a jikinsa.

Da akwai hanyoyi masu dama dake haifar da gajiya musamman a jikin dan adam musamman ma ga mutumin da mu’amalansa ko harkarsa na yau da kullum na bukatar kazar-kazar.

Bama sai ga wanda yayi wani aiki mai karfi ba, zama kawai dama kwanciya suma suna iya haifar da gajiya a jikin mutum.

Maza magidanta a kowani lokaci suna cikin gajiya saboda yadda a kullum suke fafutuka wajen yadda zasu kula da iyalansu. Hakan yasa a kowani lokaci suke bukatar sauke wannan gajiya domin samun karfi a kuzari a tare dasu. Wannan yasa ya kuma zama wajibi ko wacce mace ta iya sanin yadda zata iya warware gajiyar da mijinta ya debo daga wajen harkokinsa.

Da farko ya kamata ki fahimci wani irin gajiya ma mijinki ya shigo dashi gida domin sanin yadda zaki warware masa shi.

Akwai gajiya ta kwakwaluwa, wanda sanadiyar bacin rai ko rashin barci kan iya kawosu. A irin wannan yanayi mijinki bai bukatar yawan magana ko hayaniya. Kamata yayi ki fara kawo masa abu mai zafi na sha kamar shayi idan mai bukatar shayi ne. Idan kuma ba hakan ba ruwan sha mara sanyi soasi shi ya kamata ya soma sha kamin cin wani abu mai nauyi.

Kada ki bar yara sun dameshi a irwannan yanayin ko da kuwa shi yake bukatarsu. Da zaran sun gaisa ko suyi masa maraba ki musu umurnin barinsa ya samu natsuwa.

Wanka da ruwa mara sanyi sosai kuma ba mai zafi shine abunda oganki yake bukata a wannan lokacin. Ki tabbatar da cewa wayansa yana kashe ko baya kuwa a lokacinda yaci abinci zai kwanta. Kada ki yawaita karan radiyo ko talabijin a lokacin da yake kwance.

Shi gajiya na kwakwaluwa yafi gajiyar gabban jiki hadari. Ganin yadda kwakwaluwa yake da tasiri a jikin mutum, da zaran anyi wasa dashi ana iya fiskantar bambam matsalar kwakwaluwa.

Shi dai maganin gajiyar kwakwaluwa shine barci mai nauyi cikin natsuwa da samun kwanciyar hankali.
Zamu Ci Gaba….
Tsangayar Malam

Back to top button
error: Content is protected !!