Lilin Baba Da Ummi Rahab Suna Daf Da Zama Ma’aurata
Abu Kamar Wasa, Karamar Magana Ta Zama Babba! Saura Kiris Lilin Baba Yayi WUFF! Da Ummi Rahab, Soyayya Wasa Wasa Gashi Yanzun Tana Daf Da Kaisu Ga Aure, Idan Baku Manta Ba. Shi Lilin Baba Ya Fara Haduwa Da Ummi Rahab Ne Tun Bayan Rigimar Data Kaure Tsakaninta Da Ubangidanta.
A Inda Daga Bisani Ne Bayan An Sami Rigimar Sai Ta Kwashe Kayanta Daga Gidan Tsohon Ubangidan Nata Zuwa Wajen Lilin Baba, Haduwarsu Keda Wuya Sai Ya Fara Daurata Cikin Wannan Shahararren Shirin Nasa Mai Suna WUFF! Ana Tsaka Da Hakane Kuma Sai Akaji Labarin Soyayyar Tasu.
https://www.instagram.com/p/CeeDLGpIVfg/?igshid=YmMyMTA2M2Y=
Wasa Wasa Kawai Sai Muka Fara Samun Labarin Wai Neman Aurenta Lilin Baba Yakeyi. Karfa Ku Manta, Ummi Rahab Ta Taso Hannun Adamu Zango Na Tsahon Shekaru Koma Sha, Daga Baya Ya Bayyana Kudirinsa Kanta A Inda Ya Bayyana Cewa Yana Son Aurenta. Ita Kuma Ummin Ta Bayyana Cewa Bat Da Ra’ayin Aurensa.
Wannan Ne Dalilin Daya Fara Raba Kawunan Ita Ummin Da Ubangidan Nata. Sai Dai Kwata Kwata Bai Wuce Yan Watanni Ba Da Haduwarsu Da Lilin Baba Har Zaiyi WUFF! Da Ita. Wannan Rabo Da Yawa Yake.
https://www.instagram.com/tv/Ceb6ZL-IG5A/?igshid=YmMyMTA2M2Y=
Duk Da Cewa Mutane Da Dama Suna Ganin Ita Yarinyar Kamar Ba Kalarsa Bace, Domin Tana Da Kyau Sosai Fiye Da Tunani, Gata Kuma Karamar Yarinya.
Zuwa Yanzun Dai Shirye Shirye Yayi Nisa. A Inda Yanzun Kawai Ya Rage Asha Biki Nan Da Yan Kwanaki Kadan Masu Zuwa. Bikin Nasu Zaizo Cikin Watan Shida Ranar 18 Ga Wata. Cikin Garin Kano.







