E News

Likitoci Sun Sami Nasarar Raba Tagwayen Da Aka Haifa A Manne

Likitoci A Riyadh Sun Sami Nasarar Raba Tagwayen Da Aka Haifa A Manne Da Juna Ƴan Asalin Najeriya

A wani ci gaba mai cike da ban al’ajabi a fannin likitanci, tawagar wasu likitocin Saudiyya masu aikin tiyata a karkashin jagorancin yariman Saudiya mai jiran gado, Mohammed bin Salman bin Abdulaziz, sun kammala aikin tiyátar raba wasu tagwayen ‘yan Najeriya biyu, Hassana da Husaina, a asibitin kwararru na Sarki Abdullah da ke birnin Riyadh.

Tagwayen wanda aka haifa a Nijeriya, sun isa birnin Riyadh a ranar 31 ga Oktoba, 2023, inda aka gudanar da gwaje-gwaje na musamman da ke wuraren da za a bi yayin gudanar da aikin don raba su, wanda ya hada da duba ƙashin ƙugu da ƙananan kashin baya da ƙananan jijiyoyi.

Back to top button
error: Content is protected !!