Kannywood

Lawal Ahmad Ya Mika Sakon Godiya

Cikin Kuka! Lawal Ahmad Da Sauran Manyan Jaruman KannyWood Sun Mika Sakon Gaisuwarsu Ga Mutanen Dasu Jajanta Rasuwar Darakta Malam Nura Mustapha Waye, Wanda Allah Ya Karbi Rayuwarsa Ranar 3 Ga Watan 7, Shekara Ta 2022.

Har Yanzun Anata Jimamin Marigayi Nura Mustapha Waye, Inda Yaketa Samun Shaidar Arziki, Daga Bangarori Da Dama, Bangaran Abokan Aikinsa Na KannyWood, Bangaren Mutanen Da Yake Mu’amala Dasu, Bangaren Iyalansa, Bangaren Masu Kallo. Har Ta Kama Daga Bangaren Malamai Ma,

Mutuwar Tasa Tasa Jikin Jaruman KannyWood Da Dama Yayi Sanyi, Sakamakon Yadda Mutuwar Tazo Masa Lokaci Guda, Jarumai Da Dama Ne Su Halarci Ta’aziyyar Mamacin, Inda Kowa Ya Bayyana Shaidar Arziki Kan Marigayin.

Lawal Ahmad Ya Fashe Da Kuka Yayin Tura Nashi Ta’aziyyar, Inda Ya Bayyana Godiyarsa Ga Mutanen Dasu Tura Musu Sakon Ta’aziyya, Inda Ya Kara Bayyana Rashin Nura Mustapha A Matsayin Babban Rashi. Suma Manyan Jaruman KannyWood Irinsu Lawal Ahmad, Ali Nuhu, Sani Danja Da Kuma Yakubu Muhammad Sun Bayyana Irin Nasu Ta’aziyyar.

Back to top button