E News

Laluran Dake Damun Murja Ibrahim Kunya

Shin Kunsan Cutar Dake Sa Murja Ibrahim Kunya Ke Rashin Hankali Da Abubuwa Marasa Kan Gado Kuwa? Ga Nazarin Da Wani Masani Ya Fitar A Kanta!

Murja Ibrahim kunya

MURJA IBRAHIM KUNYA

Na daɗe ina tunani akan lamarin Murja Ibrahim kunya. Amma da farko kamar yadda nasha faɗawa mutane cewar ni ba likita bane, ni paramedic (nurse) ne ni, amma kuma ina dab da kammala karatuna a matsayin “Healthcare administrator”. Saboda haka ina da alaƙa sosai da harkar lafiya daidai gwargwado.

Wannan baiwar Allah Murja, ba shakka alamu na nuna ba daidai take ba, ina nufin akwai yuwuwar tana da “mental health issues”. Idan kai duba da irin yadda take gabatar da harkokinta da suka sabawa yanayin zamantakewa irin tamu, da yin abinda bai kamata ba a matsayinta na ƴa mace, kamar rashin jin kunyar al’umma, da yin “magana on top of magana” babu ƙauƙauta duk alamu ne dake nuna akwai matsala a tare da mai yin haka.

To a gaskiya, watakila, Murja akwai yuwuwar ɗayan abu uku a tare da ita:

Under the influence of drugs’.

Watakila abinda take yi, tana yin sane Wanda in bata sha ba, to zaka sa me ta, cikin nutsuwa, kunya da kamun kai.

Manic Personality Discorde 

Wata larurace ta kwakwalwa wacce mai fama da ita kan kasance a ‘high mood’, yana jin sa da energy da yawa a tare dashi, yawan magana, saurin magana, rashin bacci sosai, sannan abubuwa da yawa na iya dauke hankalin mutum (distractibility), dss.

Psychopathic personality disorder (psychopathy)

shima wannan neuropsychiatric disorder ne wanda ke tattare da rashin iya sarrafa ’emotion’ ga mai fama dashi, karancin tausayi, da rashin damuwa da kula da dabi’unka (poor behavioural control). Masu wannan matsalar sukan kasance masu wahalar sha’ani, wato ba’a samun kansu ta sauki, basa iya maintaining relationship, sukan zama antisocial, kai har sukan kasance masu ‘criminal behavior a wasu lokutan.

Na san ita al’umma irin tamu idan ba mutum ta gani tuburan yana nauka ba, ba kasafai suke yadda mutum nada matsalar kwakwalwa ba, musamman idan zai yi wanka ya fito tsaf dashi, koma ace shine ‘breadwinner’ a family. Saboda haka babu mai iya kaishi ko ce masa yaje asibiti.

Duk wannan ya karanta wannan maganar data faɗa a ƙasa, yasan lalle yarinyar nan ba ƙalau take ba domin maganar ta sabawa hankali, addini, da tsarin zaman takewarmu.

Saboda ya kamata danginta su fahimci lalle tana bukatar ganin likita domin binciken halinta saboda lafiyarta kamar yadda ƴan uwan Alhaji Rufa’i Billgate suke kaishi asibiti dan nema masa lafiya.

Daga Shafin Jaafar A Sarki

Back to top button
error: Content is protected !!