Kannywood

Kyawawan ‘Yan Matan Kannywood Da Har Yanzu Ba Su Yi Aure Ba

Jaruman wadanda suke da mutukar kyau ga kuma tarin masoya masu yawa, amma har yanzu ba aji suna yin maganar aure ba

Wannan dalili ne yasa wasu mutane ke yi musu kallon ‘yan iska wasu ma suke kiransu da karuwai

A yayin da mutane ke ta fa man rububi domin samun shiga a wajen fitattun jaruman na masana’antar Kannywood, sai gashi su kuma jaruman ba wannan ne a gabansu ba, domin kuwa yawancinsu sun saka sana’arsu ne a gaba da kuma kasuwancin da suke yi domin dogaro da kai.

Wannan dalilin ne yasa mutane da yawa ke yiwa jaruman wani kallo na daban, inda wasu ke musu kallon fitsararru, ‘yan iska, wasu ma suna kiransu da suna karuwai, saboda sun ki tsayawa su yi aure.

Fitattun jaruman wadanda suke da kyau, kwalisa, ga kuma tarin masoya, har yanzu dai ba aji suna maganar aure ba, hakan yana da nasaba da abinda wasu ke cewa na suna ruwan ido, wasu kuma sunce suna jiran zabin Allah ne.

Wannan dalili ne yasa jaridar Legit.ng ta binciko muku jerin kyawawan jaruman guda takwwas wadanda har yanzu basu yi aure ba.

1. Hadiza Gabon

2. Amina Amal

3. Maryam Yahaya

4. Aisha Tsamiya

5. Nafisa Abdullahi

6. Rahama Sadau

7. Fati Washa

8. Fati Shu’uma

Back to top button
error: Content is protected !!