Kannywood

Kwankwasiyya: Ahmed Lawan ya baiwa jarumi Mustapha Nabruska mukami

Sashin labarai na kamfanin haska fina-finan Hausa na Northflix, ya bayyana cewa Mustapha Nabraska ya samu mukami a ofishin Ahmed Lawan

– A ranar Larabar da ta gabata ne aka bayyana cewa, shugaban majalisar dattijai ya ba jarumin mukamin mai bashi shawara ta musamman

– Kamfanin ya tabbatar da cewa, an ba shi wannan mukamin ne saboda cigaban al’umma tare da habaka ta
Sashin labarai na kamfanin haska fina-finan Hausa na Northflix ya bayyana cewa, Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawal ya ba wa jarumin fina-finan Hausa Mustapha Nabraska mukamin mai bashi shawar na musamman.

A ranar Larabar da ta gabata ne jarumin fina-finan barkwancin, ke bayyanawa a shafinsa na sada zumunta na Instagram inda yake shaidawa duniya wannan albishir.

Ya wallafa rubutu kamar haka: “Dukkan godiya ta tabbata ga Allah. Mun shiga aiki gadan-gadan a majalisa. Nayi nasara zama mai bada shawara na musamman na shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan.”

Kamar yadda gidan rediyon Dabo FM ya ruwaito, ba a tabbatar da hakan ba don bata samu zantawa da jarumin.

Northflix ta ce: “Sanata Ahmed Lawan ya ba shi wannan mukamin na mai ba shi shawara ne kan harkokin ci gaban al’umma.”

Back to top button
error: Content is protected !!