Kwalara Ta K@she Mutum 29 A Legas
Kwalara Ta K@she Mutum 29 A Legas, Yayin Da Ake Zargin Sama Da Mutum 500 ne suka Kamu Da Cutar A Jihar.
A Jihar Ogun Mai Makwabtaka Da Legas, Mutum Daya Ne Ya R@su Yayin Da Kusan Mutum 30 Ake Zargin Sun Kamu Da Cutar.
Tsaftar Jiki Da Muhalli Na Sawun Gaba Wajen Rigakafi Da Kare Yaduwar Bazuwar Cutar Kwalara, Don Haka Masana Kiwon Lafiya Ke Bai Wa Jama’a Shawarwarin Da Suka Hadar Da Kula Da Tsafta, Wanke Hannuwa Bayan An Shiga Bayi, Tsaftace Ruwan Sha, Kula Da Dakin Dafa Abinci, Wanke Kayan Lambu Kafin Aci, Sannan Idan Mutum Ya Kamu, Ayi Gaggawar Garzayawa Da Shi Asibiti.
Mahukunta A Fannin Kiwon Lafiya A Legas Sun Ce Rashin Kai Marasa Lafiya Asibiti A Kan Lokaci Na Cikin Abun Da Ya Sanyan Alkaluman Wadanda Suka R@$u Ya Haura, Sun Ce Yawancinsu An Kaisu Asibiti A Makare Lamarin Da Ya Sanya Suka Galabaita Kodarsu Ta Daina Aiki.
A Jihar Ogun Mahukunta a Fannin Kiwon Lafiya Sun Ce Jerin Farko Na Wadanda Suka Kamu Da Cutar Sun Yi Bulaguro Zuwa Legas, Kuma Cikinsu Wasu Sun Ce Sun Sha Kunun Aya A Legas.
Masana Kiwon Lafiya Sun Ce Ana Samun Karuwar Bazuwar Kwalara A Lokacin Damuna, Kuma Cutar Na Yin Kyamari Ne A Yankuna Masu Zafi.
Shin Kuna Sane Da Rahotan Bullar Cutar Kwalara A Najeriya?
Wani Matakin Kariya Kuke Dauka?