Kannywood
Kusani A Addu’a Allah Yaban Mata Ta Gari – Adam A Zango
Ku Sakani A Addu’arKu Allah Ya Bayyanamin Matar Da Zan Aura Wacce Mutuwa Ne Kadai Zai Rabamu – Adam A Zango
Fitaccen Jarumi a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A. Zango ya nemi al’ummar musulmai su taya shi da addu’a Allah Ya ba shi matar aure wacce ba za su taɓa rabuwa ba har abada.
Adamu A. Zangon Ya bayyana hakan ta cikin shafinsa kamar yadda ya ce:
“Dan Allah ku saka ni a addu’arku Allah Ya bayyana min matar da zan aura a cikin wannan wata mai albarka Daren Lailatul Qadir. Matar da zan yi alfahari da ita Duniya da Lahira. Allah Ya sa mutuwa ce kaɗai za ta raba ni da ita”. Ya ce.
Idan jama’a ba su manta ba, an sha ruwaito labaran mutuwar aurarrakin da Jarumin yayi wanda har ta kai ga mutane na jifansa da “mai auri saki” wanda shi da kansa ya sha fitowa kafar sadarwa ta zamani yana kare kansa daga zarge-zargen da al’umma ke yi masa tare da bayyana hakan a matsayin wani babban abin baƙin ciki da damuwa da ke damunsa sosai.