Kungiyar yan Fim ta bayyana matakin da za ta dauka a kan Maryam Booth
Biyon bayan bullar bidiyon tsiraicin fitacciyar jaruma Maryam Booth, shugaban kungiyar jaruman fina finan Kannywood, Alhassan Kwalle ya bayyana cewa kungiyarsu ba za ta sallame ta daga cigaba da harka a masana’antar fina finan Kannywood ba.
Daily Trust ta ruwaito Kwalle ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da yayi da wakilinta a ranar Litinin, 10 ga watan Feburairu, inda yace abinda ya faru da Maryam Booth ba daidai yake da na Maryam Hiyana da aka taba yi shekarun baya ba.
Saboda a cewarsa, wannan bidiyo na tsiraicin Maryam Booth an yada shi ne don a ci zarafinta tare da wulakanta ta, haka zalika ya bayyana damuwarsa da irin kallon da jama’a suke yi ma yan fim, don haka yace kungiyarsu za ta cigaba da baiwa Maryam goyon baya har sai an yi mata adalci.
“A matsayina na jagora a masana’antar Kannywood, na kan yi mamakin yadda jama’a ke kallonmu, nan bada jimawa ba aka samu irin wannan bidiyon kafin na Maryam Booth, amma bai yi yawo a cikin jama’a ba kamar wannan.
“Kowa ya sani abin da aka yi ma yarinyar nan cin zarafi ne domin a ci mutuncinta kuma a bata mata suna, ba wai tana daukan fim bane ko wani abu ba, ta yi kokarin daukan mataki, amma mutumin daya dauki bidiyon sai ya yi kamar ya goge.
“Tsawon shekaru uku ya yi yana amsan kudi a hannunta da sunan zai fitar da bidiyon, har zuwa ranar Juma’a daya fitar da shi. Ya kirata wai zai kai babarsa asibiti don haka yana son ta bashi kudi, amma ta ki, wannan ne dalilin da yasa ya saki bidiyon.” Inji shi.
Shi ma a nasa jawabin, shugaban hukumar tace fina finai ta jahar Kano, Ismail Afakallahu ya bayyana cewa damuwarsu kawai abinda aka dauka a fim domin jama’a, ba wai wani dan karamin bidiyo da aka dauka don cin zarafi ba.
Afakallau yace koda yake bai kalli bidiyon ba, amma daga abubuwan da mutane suke fadi ba wani abu bane da aka yi da nufin bidiyon lalata ba, don haka babu wani hukuncin da zasu dauka a kan yarinyar.