K*san Gillan Da Su Tada Hankula A Arewacin Najeriya
K*san da ake zargin wata matar aure ta yi wa wani matashi a Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ya jawo ce-ce-ku-ce sakamakon yadda ake samun bayanai daban-daban da suke fitowa masu daure kai.
Tuni rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da kama Hafsat Surajo mai shekara 25 kan zargin k*she Nafiu Hafiz mai shekara 38.
‘Yan sandan sun bayyana cewa Hafsat ta amsa laifin da ake zarginta da shi inda ta ce ta c*ccaka masa w*ƙa a sassan jikinsa daban-daban.
Sai dai a tattaunawar da ‘yan jarida suka yi da mahaifin marigayi Nafiu, ya ce yana fata hukumomi za su dauki matakin da ya dace da kuma yin adalci don kada lamarin ya kasance kamar yadda wasu irinsa suka kasance a baya.
A shekarun baya an samu irin wadannan lamura sau da dama a Nijeriya musamman a Jihar Kano, sai dai har yanzu babu wani kwakkwaran hukunci da aka zartar game da k*she-k*shen da aka yi.
Maryam Sanda
A watan Nuwamban 2017 aka zargi Maryam Sanda da laifin k*she mijinta mai suna Bilyaminu Bello, wanda da ne ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP Halliru Bello.
Rahotanni a lokacin da lamarin ya faru sun ce Maryam ta samu sabani da mijin nata ne wanda hakan ya kai ga ta c*ka masa w*ka.
Bayan faruwar lamarin aka gurfanar da Maryam a gaban kotu inda alkali ya yanke mata hukuncin k*sa a shekarar 2020 bayan samunta da laifin k*she mijinta.
Sai dai daga baya Maryam ta daukaka kara inda ta zargin alkalin kotun da shari’a bisa son rai. Har zuwa yanzu babu wani karin bayani game da ci gaban shari’ar Maryam.
K*san Hanifa
K*san Hanifa wadda yarinya ce mai shekara biyar a Kano ya yi matukar tayar da hankalin jama’a sakamakon yadda lamarin ya kasance mai ban tausayi da takaici.
Bayan k*san Hanifa, Babbar Kotun Kano ta yanke wa malaminta Abdulmalik Tanko hukuncin k*sa bayan samunsa da laifin g*rkuwa da Hanifa da l*ifin k*santa da kuma laifin kitsa yadda za a yi g*rkuwa da ita.
Tun da farko malamin na su Hanifa ne ya hada kai da wasu domin s*ce ta inda daga baya ya k*she ta sannan ya binne ta a cikin wani buhu.
Ummita da Dan China
A shekarar 2022 ne aka zargi wani dan kasar China mai suna Geng Quangron da k*she budurwarsa mai suna Ummulkulsum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita.
Shi ma wannan lamarin ya tayar da kura.
Daga TNTHausa
Ni ina ganin ba bukata ku dinga sauya kalmomi irin kisa, da wuka, da caka, kamar yadda ku ke yi nan. Wannan website ne na labarai, kuma domain din ku ne, labarun ku ne, ba kan website din wani za ku saka ba. To ina dalilin cire haruffa?
Akwai Kalaman Da Idan Anyi Amfani Dashi Muna Samun Qalubale Daga Kamfanin Dake Bamu Talluka, Akwai Kalamai Dasu Hatamta Amfani Dasu,
Mungode Da Shawara Da Kuma Kulawa