Labarai
Kotu Taci Tarar Gwamnatin Kano Naira Miliyan 10
Kotu Taci Tarar Gwamnatin Kano Naira Miliyan 10,Ta Ce a Bai Wa Sarkin Kano Aminu Ado, Domin A Tauye Masa Haƙƙi
Babbar Kotun Tarayya ta ba da umarni ga gwamnatin jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya ta biya diya miliyan 10 ga Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero saboda abin da ta kira take masa hakki.
Kotun tace umarnin da gwamnatin Kano ta yi na a kama sarkin ya saba wa dokar kasa matakin da ya tilasta masa zaman gida, da take masa hakki na dan Adam da watayawa.
Mai Shari’a Simon Amobeda ya fitar da wannan hukunci inda yace ahir din babban mai gabatar da kara da ‘yansanda ko wasu su yi yunkurin kama sarkin.