Labarai

Kotu Ta Yanke Ma Maryam Sanda Hukuncin Kisa

Akalin babbar kotun a Abuja, mai shari’a Yusuf Haliluya, ya zartar wa Maryam Sanda, matar da ake zargi da kashe mijinta a 2017, hukuncin kisa ta hanyar rataya.


An soma zargin ta ne tun a Nuwamban 2017 da laifuka biyu da suka hadar da kashe mijin nata mai suna Bilyaminu Bello, wanda da ne ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa Haliru Bello.


A watan Disamban 2017 ne dai aka gurfanar da Maryam Sanda bisa zargin kisan mijin nata.

A lokacin da yake yanke hukuncin, alkalin ya ce an samu dukkanin wasu shaidu da suka tabbatar da cewa Maryam ce ta aikata wannan laifi.

Ya kuma yi watsi da ikirarinta na cewa mijin nata ya fadi ne kan fasasshiyar tukunyar Shisha, abin da ya janyo mutuwar tasa.

Ya kuma bayyana cewa hujjojin da aka gabatar sun gamsar da kotu cewa ta caka wa mijin nata wuka ne yayin da fada ya kaure a tsakaninsu

A lokacin da alkali ya zartar da hukuncin wadda ake tuhuma ta yi kokarin rugawa domin guduwa daga zauren kotun sai dai jami’an tsaro sun rike ta.
BBChausa

Back to top button
error: Content is protected !!