Kotu Ta Tsare Dan Jarida Saboda Ya Caccaki Gwamnatin Abba Gida Gida
Kotu Ta Tsare Dan Jarida Saboda Ya Caccaki Gwamnatin Abba Gida Gida A Facebook
Wata kotun majistare da ke zaman ta a Kano ta tsare Muktar Dahiru, dan jaridan da ke aiki a gidan radiyon Pyramid FM da ke karkashin gidan radiyon Najeriya na kasa na FRCN bisa zarginsa da yin wani rubutu a Facebook ci mutuncin Abba gida gida, wato gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.
A ranar Alhamis ne aka kama Dan Jaridar,wanda aka gurfanar a asirce a gaban kotun majistare 24 da ke Gyadi Gyadi, inda ake tuhumarsa da laifin hada baki, bata sunan mutum, da kuma batanci da gangan.
Alkalin kotun, Ummah Kurawa, ta tisa keyar Dahiru zuwa gidan gyaran hali, har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraron karar neman belinsa a ranar 3 ga watan Satumba.
An ce dan jaridar ya yi hira da wani dan siyasan adawa a wata hira da aka watsa a cikin sautin murya yana zargin gwamnan da cin hanci da rashawa.
Dan siyasar na adawa ya bukaci gwamnan da ya baiwa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na tarayya damar gudanar da bincike kan badakalar kamfanin da ake zargi da badakal kudin kananan hukumomi da sunan sayan magunguna, maimakon hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano wato PCACAC.