Kotu Ta Hana Aminu Ado Bayero Kiran Kansa Sarki,
Kotu Ta Hana Aminu Ado Bayero Kiran Kansa Sarki, Shida Sauran Sarakuna 4 Da Aka Tuɓe
Babbar kotun jihar Kano mai lamba 17, ƙarkashin jagorancin mai shari’a Amina Adamu Aliyu, ta dakatar da Aminu Ado Bayero da wasu ƙarin sarakuna hudu da aka tsige daga sarautar Bichi, Rano, Gaya, da kuma Ƙaraye a matsayin sarakuna har abada, inda ta umarce su da kada su saki kiran kansu da sarki.
Da take zartar da hukuncin a ranar Litinin, kotun ta kara da cewa Sarkin Kano na 15 da wasu sarakuna hudu, da hadimai, masu zaman kansu da kuma duk wani mutum da suka naɗa su guji bayyana kansu a matsayin sarakunan Kano, Bichi, Gaya, Rano, Karaye.
Gwamnatin jihar Kano dai ta shigar da ƙara ne inda ta buƙaci kotun ta daƙatar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da wasu sarakunan Karaye da Bichi da Rano da kuma Gaya daga gabatar da kansu a matsayin sarakuna.
Gwamnatin ta kuma baiwa Sarakunan da aka tsige sa’o’i 48 da su fice daga fadarsu bayan an sauke su.
Sai dai kuma mai shari’a Amina Adamu Aliyu, yayin da take yanke hukuncin, ta ce batun korar tsohon sarkin, Aminu Ado Bayero daga fadar sa ta Nassarawa lamari ne na kotun haya, don haka ba hurumin ta bane.
Amma a hukuncin da ta yanke, Alkalin ya umarci Mai Martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da wasu mutane hudu da su gaggauta mika dukkan kayayyakin tarihi na Masarautar ga gwamnati da kuma sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Mai shari’a Amina Adamu Aliyu, ta kuma ce Majalisar Masarautar Jihar da ta soke dokar shekarar 2024, an yi ta ne kamar yadda doka ta tanada a sashe na 4 na kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya.
Daga nan sai ta yanke hukuncin cewa amincewar da Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf ya yi wa dokar ya yi daidai da tsarin mulkin Tarayyar Najeriya.