Labarai

Kotu Ta Bada Belin Tsohon Ministan Jiragen Sama, Hadi Sirika

Kan tuhumar Cinye Bilyan N19.4bn: Kotu Ta Bada Belin Tsohon Ministan Jiragen Sama, Hadi Sirika

Mai shari’a Suleiman Belgore na babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Garki Abuja ya bayar da belin tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da ake tuhumarsa da laifin zamba har naira biliyan goma sha tara da miliyan hudu.

Mai shari’a Belgore ya bayar da belin tsohon Ministan a kan kudi Naira Miliyan Dari (N100,000,000) da kuma mutum biyu wadanda za su tsaya masa. Daya daga cikin wadanda za su tsaya masa dole ne ya mallaki kadarorin da ke karkashin ikon kotu.

A yau ne aka gurfanar da Hadi Sirika da dan uwansa a gaban kuliya dangane da badakalar kwangilar da ta kai Naira biliyan 19.4.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika bisa zargin badakalar kwangila.

Sirika, tare da rakiyar dan uwansa Ahmad Abubakar Sirika da Enginos Nigeria Limited, wani kamfani mallakin Abubakar, an gurfanar da shi a hukumance da tuhume-tuhume guda 10 da aka yi wa kwaskwarima a ranar 13 ga watan Mayu, sannan aka gabatar da shi a hukumance ranar 14 ga Mayu, 2024.

Back to top button
error: Content is protected !!