Kannywood

Ko Tsirara Kisa Hotona, Wallahi Sai An Aura Ni – Martanin Sadiya Kabala

Wata magana da Jakadiyar tonon asiri ta yi akan Sadiya Kabala na nema ta zama rigima

Yayin da jarumar da jakadiyar suka fara shagube da gugar zana ga junan su

Jarumar dai ta mayarwa da jakadiyar wani martani mai zafi, bayan jakadiyar ta wallafa wani rubutu a kanta

Ba yau ne kadai aka saba kace-nace tsakanin jaruman fim musamman mata da jakadiyar tonon asiri ba, wacce tayi suna sosai a shafin Instagram wajen tona asiri tare da bankado duk wani abu na Allah wadai da jaruman fim suke yi tana yadawa duniya tana gani.

Duk da dai har ya zuwa yanzu dai an kasa gano ko wacece jakadiyar ko kuma wanene jakadiyar, saboda wasu mutanen na tunanin cewa jakadiyar namiji ne ba mace ba, amma dai koma dai wanene ko wacece, basa kyautawa jaruman fim din. Abin na jakadiyar ba wai ya tsaya akan jaruman fim bane kawai hatta ‘ya’yan manya mata ‘yan bariki da dai duk wani mai yin katobara a shafukan yanar gizo idan har hoto ko bidiyon shi ya ci karo da jakadiya to zance ya kare.

A wanna karon dai rikici ne ya sake hado su da abokiyar fadanta wato Sadiya Kabala wacce a kwanakin baya jakadiyar ta zarge ta da kalmar madigo, saboda ta dauki hoto da jaruma Maryama Yahaya, inda aka nuno su sun naniki juna.

Duk da dai wannan karon bata jefeta da wata mummunar kalma kamar waccan ba, saboda ta sanya hijabi kawai dai tayi mata gugar zana ne, amma dai hakan bai hana Sadiya Kabala maida mata da martani ba, inda bayan jakadiyar ta wallafa hoton Sadiya cikin shiga ta kamala da hijabi a kasa ta rubuta:

“Wallahi da zaki ma kanki fada ki koma sa hijab da kinfi kyau sosai baki ga yadda hijab dinnan yayi miki kyau ba, saboda rashin mutunci har zuwa wajen gym kike yi, hmmm Allah ya shiryeki Sadiya Kabala.”

Wannan ya sa Sadiya ta mayar mata da martani da cewa:

Dama idan ruwa ya karewa dan kada sai ya koma tunkuri, ashe kina nan jiya ko na gama cigiyarki na jiki shiru kwana biyu, dama na kosa na samu masoya miliyan daya a taimaka a nemo mai zafi a dora domin wannan ba zai saka mutane su biyo ni ba. Dan Allah ki nemo mai zafi ki saka.

Iyayen leke-leke ke kofa a tsirara zaki samu wallahi sai mun sai mun auru dan ba kanmu farau ba kuma ba kanmu karshe ba.”

Back to top button
error: Content is protected !!