Kannywood

Ko Meyasa Matan KannyWood Su Koma Yin Auren Sirri?

Ko Menene Dalilin Da Yasa Matan KannyWood Su Koma Yin Auren Sirri? Akasin Yanda Abun Yake A Baya. Kamar Yanda Muka Sani, A Shekarun Baya Idan Jarumi Ko Jarumar Fim Zasuyi Aure.

Akan Sha Biki Ne Sosai, Domin Akanyi Bukukuwa Kala Iri Daban Daban Kafin Akai Ga Anje Ranar Daura Auren, Sai Dai Zuwa Yanzun Wannan Lamarin Ya Zama Tsohon Zance.

Daga Cikin Shekarar Data Gabata Zuwa Wacce Muke Ciki Na 2022, Jarumai Musanman Mata Na Cikin Masana’antar KannyWood Sunkai Su Biyar Zuwa Sama Wanda Suyi Auren Sirri.

Akwai (Zahra Diamond,) Wacce Rana Guda Kawai Aka Sami Labarin Tayi Aure, Sai (Maryam Yahaya) Itama Saida Aka Daura Auren Tukunna Mutane Suka Sami Labarin Cewa Ta Amarce.

Na Baya Bayan Nan Kuma Akwai Shahararrun Jarumai Guda Biyu. (Hafsat Idris Barauniya Da Aisha Aliyu Tsamiya) Da Su Amarce Kusan Rana Guda. Suma Ba.a Sami Labari Ba Sai Daga Bayan An Daura Auren Nasu.

Akwai Wata Jarumar Ba Da Ba Kowa Yasanta Ba. Mai Suna Nadiya Adamu Itama Ta Amarce Duk Cikin Sirri A Wannan Satin.

Shin Me Kuke Tunanin Yakesa Matana KannyWood Din Yin Auren Sirri?

 

 

Back to top button
error: Content is protected !!