Katin Gayyata Na Auren Maishadda Da Hassana.
MashaAllah. Katin Gayyatar Auren Abubakar Bashir Maishadda Tare Da Amaryarsa Hassana Muhammad, Inda Shahararren Producer Zai Angwance Ta Wannan Kyakykyawar Karumar Hasaana Muhammad.

Hassana Muhammad Dai Ta Kasance Daya Daga Cikin Jarumar Da Tauraruwarsu Su Haska Sosai A Lokaci Guda, Inda Taja Ragamar Wasu Manya Manyan Fina Finai Wanda Yawancinsu Sunzo Ne Karkashin Kamfanin Shi Abubakar Bashir Maishadda.
Daga Bayane Dai Shi Maishadda Ya Kuduri Aniyar Zai Aureta, Inda Gaba Daya Ya Hanata Fitowa A Cikin Fina Finai. Lokaci Guda Akaji Karumar Tayi Shiru.
Ko A Shafukan Sada Zumunta Ma. Ba.a Fiya Jin Duriyarta Ba, Yau Dai Maishadda Ya Fitar Da Sanarwar Ranar Da Zai Angonce Tare Da Amaryar Tashi.
Ranar Lahadi Sha Uku Ga Watan Uku Shekara Ta Dubu Biyu Da Ashirin Da Biyu. 13/03/2022, Inda Za.a Daura Auren A Masallacin Murtala Cikin Garin Kano, Da Misalin Karfe 11. Na Safe.
Muna Fatan Allah Yasa Ayi Lafiya Ya Kuma Basu Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali.