Karuwanci ba haramun ba ne a Abuja – Kotu
Wata kotu a Najeriya ta yanke hukuncin cewa ‘karuwanci’ ba laifi ne ba, kasancewar babu wata doka da ta haramta shi.Mai shari’a Binta Nyako ta babbar kotu a Abuja, ta nemi a biya diyya ga mata 16 da aka kama bisa tuhumar ‘karuwanci’ a 2017.
Wannan ne karon farko da wata kotu a Najeriya ta yanke hukunci kan halascin ‘karuwanci’.
Lauyan da ke kare matan, Babatunde Jacob ya shaida wa BBC cewa kotun ta ce jami’an tsaro sun keta hakkin wadanda yake karewa kasancewar sun kutsa cikin gidajensu suka kuma kama su bisa zargin karuwanci.
Masana shari’a dai a kasar na ganin wannan hukunci ka iya yin tasiri ga ‘yan Najeriya wadanda suka fi kowace al’umma yawa a nahiyar Afirka.
Jami’an tsaro a Najeriya dai sun saba kama da tsare mata masu zaman kansu.Yayin wani samame a watan Mayu na 2019, an kama mata fiye da 60 bisa zargin yin ‘karuwanci’ a Abuja.
Da dama daga cikin matan sun yi ikrarin cewa an ci zarafinsu da zamba cikin aminci sannan an kunyata su a bainar jama’a.Labarai masu alaka