Labarai
Kanu Ya Saduda Ya Nemi Sulhu Da Gwamnatin Najeriya
Jagoran ‘Yan Fafutukar Kafa Ƙasar Biya fara Ya Saduda Ya Nemi Sulhu Da Gwamnatin Najeriya
Shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu a ranar Laraba, ya bayyana aniyar neman tattaunawa da gwamnatin tarayya.
Kanu ya tsaida matakin da ya dauka na tattaunawa da gwamnatin tarayya a karkashin sashe na 17 na dokar babban kotun tarayya.
Hukumar DSS ta tsare shugaban kungiyar ta IPOB tun a shekarar 2021 inda aka sake kama shi a Kenya aka mayar da shi Najeriya.