Kannywood Tayi Babban Rashin Jagora
Allah ya yi wa fitaccen tsohon jarumin masana’antar Kannywood, Daudu Galadanci, wanda aka fi sani da Alkalin Kuliya rasuwa.
Tsohon jarumin ya rasu ne a ranar Laraba, 13 ga watan Mayu, da dare.
Za a yi jana’izarsa kamar yadda addinin Islama ya tanada a Galadanci da ke birnin Kano da karfe tara na safiyar Alhamis, 14 ga watan Mayu.
Sakon mutuwar nasa na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban jarumin masana’antar, Ali
Nuhu, ya wallafa a shafinsa na Instagram.
Ya ci gaba da wasanni har zuwa zamanin fina-finan Hausa na Kannywood inda aka dama da shi.
Mutuwarsa na zuwa ne yan makonni bayan mutuwar wani jarumi, Ubale Ibrahim wanda aka fi sani da wanke-wanke.
Mutuwar ta girgiza ‘yan fim ɗin Hausa, musamman da yake ba a ji labarin ko ya yi rashin lafiya ne ba.
Ya rasu ne a safiyar ranar 1 ga watan Mayu, inda aka yi jana’izar jarumin a gidan sa da ke unguwar Rangaza da ke Ƙaramar Hukumar Ungoggo a cikin garin Kano, kuma aka binne shi a makabartar Tudun Murtala.
Dimbin ‘yan fim da sauran jama’a sun halarta.
Cikin manyan ‘yan fim da su ka halarta akwai aminan marigayin, wato Sani Musa Danja, Ali Nuhu, Yakubu Muhammad, sai kuma Mustapha Nabraska, Abdul Amart, T.Y. Shaban, da Jamilu Ibrahim.
Marigayin, mai kimanin shekaru kusan 50, ya rasu ya bar matar sa ɗaya da ‘ya’ya shida -biyar maza ɗaya mace – da kuma mahaifin sa.
Allah ya gafarta masu, yasa sun huta, ya kyautata tamu idan ta zo.