Kannywood

KannyWood Sun Shirya Maka SarKin Waka A Kotu

Yanzu – Yanzun. Yan KannyWood Sun Shirya Tsaf Don Maka Nazir SarKin Waka A Kotu Bisa Zargin Lalata Da Mata Daya Furta Sunayi.

Hakan Na Faruwa Ne Tun Bayan Hira Da Akayi Da Baba Tambaya Na Cewa Da Tayi. Idan Nayi Fim Kwata Kwata Naira #3000 Ko #5000 Ake Bani, Hakan Ne Ya Jawo Mummunan Cece Kuce A Tsakanin Jaruman Masana’antar KannyWood Inda Nazir SarKin Waka Ya Fito Yayi Kaca Kace Da Manyan Masu Shirya Fina Finai Inda Yace Yan Fim Bakwajin Tsoran Allah – SarKin Waka

Cikin Maganganun Da SarKin Wakan Ya Fada Yace Ana Lalata Da Wasu Yan Matan Kafin A Sakasu A Cikin Shirin Fim. Sannan Kuma Masu Shirya Fina Finan Basa Biyan Jarumai Hakkinsu Kamar Yadda Yakamata.

Babban Abin Dayafi Tada Hankalin Yan Masana’antar KannyWood Shine Cewa Da Akayi Ana Lalata Dasu Kafin A Sasu A Cikin Shirin Fim.

Hakan Ne Suke Ganin Ya Dace Su Maka Shi SarKin Wakan A Kotu Domin Kazafi Da Yayi Akansu.

Sun Bukaci SarKin Wakan Da Ha Bayyanar Da Wata Ko Wani Da Akayi Lalata Dasu Kafin A Sasu A Fim,Zuwa Yanzun Dai Babu Wata Data Fito Ko A Fili Ko A Boye Ta Bayyana Cewa An Nemi Lalata Da Ita Yayin Da Ta Nemi Asata A Wani Shirin Fim.

Ga Martanin Mustapha Na Biraska Kan Wannan Lamari.

https://m.youtube.com/watch?v=LzDyKGU3lsQ

One Comment

Back to top button
error: Content is protected !!