Kalubalen Masana Kiwon Lafiya Ga Shirin LABARINA
Kalubalen Masana Kiwon Lafiya Ga Shirin LABARINA Da Martanin Marubucin Shirin
(A daure a karanta har karshe don a samu fahimta da karuwa)
Daga Dr. Ibrahim Musa
Ya kamata marubuta Labarina su karanta yarda ake genetic counseling and testing. Farko dai su fahimci yarda Hemoglobin F yake switching zuwa Hemoglobin S. Hakan zai haska musu cewa context din da suke son haskawa sunyi shi upside down.
Da farko dai AS da AS idan sukai aure matar ta samu ciki, suna da probability na samun zuria mai cutar sickle cell 25% (1:4). Kuma koda dan ko yar dake ciki tana da sickle cell ba zai zama sanadin bari (miscarriage) ba. Kuskure na farko shine nuna cewa cikin ya bare ne saboda dan su yana da sickle cell. Shi sickle cell ba matsala bace ga dan dake cikin uwa saboda a wannan lokacin duk hemoglobin dinsa F ne ko sauran embryonic hemoglobins. Sai bayan an haifi jariri da kamar wata uku zuwa shida sannan hemoglobin F zai canja zuwa hemoglobin S. A wannan matakinne kawai ciwon sickle cell yake bayyana a zahiri yayi tasiri.
Kuskure na biyu shine yarda likitan Labarina yayi counseling Mainasara. Shi counseling ana yinsa ne domin maaurata su fahimci menene risk dinsu na kamuwa da ciwo ko yada shi ga zuriar su. Abu na farko da ake koyawa counselor shine kada ya taba saka baki akan zabin da maauratan zasu yiwa kansu. Kuma maauratan ake hadawa a wuri daya ayi musu bayani gamsasshe sai ace suje suyi shawara a tsakaninsu. Kuskure ne a nuna likita ya ware miji shi kadai yace masa sai dai su daina haihuwa ko su rabu. Ba aikin sa bane wannan. Ba kuma shawara bace ta ilmi, musamman ma da sun riga sunyi aure- ba kafin aure suka zo premarital genetic counseling and testing ba.
Abinda likita zai yi a nan shine ya sanar dasu cewa suna da 25% risk na samun zuria mai sickle cell a duk lokacin da matar ta samu juna biyu. Sannan ga irin dawainiyar dake tattare da rainon mai ciwon sickle cell. Ga kuma irin abinda ya kamata daga gare su iyaye. Kamar Mainasara, tunda attajiri ne, zasu iya yin IVF ayi musu embryo selection a zabi wanda bashi da sickle cell a dasa musu. A wasu kasashen suna iya yin prenatal screening idan cikin na dauke da sickle cell suyi abortion tun yana kankani. Abu na uku, suna iya yin newborn screening idan yana da sickle cell su fara shirin yi masa stem cell transplant ko gene therapy su warkar da shi. Idan ma duk hakan ya gagara, akwai magunguna na zamani da suke karfafa lafiyar masu ciwon sickle cell- wadansu yanzu ake kan bincikensu. Dük wadannan bayanai sai an haska su ga maaurata domin aba su zabi. Kuskure ne ace ita matar ba zata haihu ba don kawai ita da mijinta suna da AS.
Da fatan za a gyara a gaba.
GA MARTANIN MARUBUCIN SHIRIN
Daga Yakubu M. Kumo
Dr. ya buɗe bayanansa kuma an ƙaru sosai, duk da dai abubuwa da yawa da ya kawo suna cikin labarin. A yanzu matsalar ta fara, da za a cigaba da bi a hankali, yawancin karatun da Dr. ya kawo za a samu a ciki, saboda dai dai gwargwado an yi bincike kafin a ɗora alkalami wajen fara rubutun, sai dai ajizanci na ɗan adam dole a sami kuskure ɗaya ko biyu, musamman da ya zamana a duk cikin crew na Labarina babu likita. Da bincike da tambaya muka dogara, matambayi kuma a wani lokacin fa ko bai ɓata ana iya ɓatar da shi.
Lallai haka ne, yiyuwar haihuwar ɗa da cutar sickle cell ga ma’aurata AS+AS 24% ne, ko 1/4 wato ɗa ɗaya cikin huɗu, amma Dr. bai bayyana cewar za a iya rashin sa’a ƴaƴan ko sun kai goma duk su zo da cutar ba, ko kuma duk su zo ba cuta ko kuma wasu su samu wasu kuma su rasa. A dalilin haka ne hatta malaman addini su ke ba da shawarar kar a yi auren ya fi ko kuma idan har an yi a rabu akan a haifi yaran su zo da ciwon, musamman da ya ke shari’a a kullum na da manufar kare rai ne (Hifz al Nafs) ko a kiyaye batar da dukiya wajen jinya (Hifz al maal).
Duk da Dr. ya ce Mainasara yana da dukiya za a iya zubar da ciki tun da wuri idan aka fahimci cikin yana ɗauke da cutar ko kuma a cire cutar tun yaron na ciki. Na so a ce Dr. ya faɗi ko akwai hatsari a yin hakan ko babu, amma dai idan aka bi labarin za a ga yadda aka kawo waɗannan batutuwan duka, ba na so na fallasa cigaban. A dai cigaba da kallo kawai.
Likita an ce ya yi katsalandan akan aikin da ba na shi ba, za a ja ma sa kunne kar ya sake shiga sharo ba shanu, duk da kuwa shi ɗin yana ganin kansa kamar ya zama ɗan uwa ko mashawarci ga Mainasara ne. Ai Mainasaran ma ya gargaɗe shi tun a wajen idan ba a manta ba. Mun gode ƙwarai da gaske Dr. Ibrahim Musa, kuma wannan bayani da ka kawo zai yi amfani ko da a ayyuka na gaba ne insha Allah. A cigaba da bi ana ba mu gyara, ma su kallo kuma suna mana uzuri.
Me za ku ce game da wannan kalubale da kuma martani da aka yi?