Ungategored

Kalubale na farko Dana Samu Farko Shiga Ta Kannywood Shine Iyayena Da Suka ki Amince Mini

Fitacciyar jarumar masana’antar Kannywood, Rukayya Umar Santa wacce aka fi sani da dawayya ta zanta da gidan rediyon Freedom

– Jarumar da aka fi sani da Rukayya Dawayya, ta ce ta samu nasarori masu dimbin yawa a shekaru 15 da ta yi a masana’antar

– Ta bayyana cewa, babban kalubalen da ta fara fuskanta shine rashin amincewar iyayenta da ta bijiro da bukatar shiga fim
Sananniyar jaruma kuma mai daukar nauyin fina-finai, Rukayya Umar Santa wacce aka fi sani da Dawayya, ta bayyana cewa ta samu nasarori masu tarin yawa a masana’antar.

Yayin wata tattaunawa da tayi da gidan rediyon Freedom, ta bayyana cewa ta samu nasarori masu tarin yawa a rayuwarta cikin sama da shekaru goma sha biyar da ta shafe a masana’antar.

Kalubale na farko dana samu farkon shiga ta Kannywood shine iyayena da suka ki amince mini
Dawayya ta ce, babban kalubalen da ta fuskanta kafin shigarta masana’atar shi ne rashin amincewar iyayenta. Domin kuwa da farko sun nuna rashin amincewarsu kafin daga bisani suka amince.

Ta kara da cewa, ta samu cigaba mai tarin yawa lokacin da tazo masana’antar da farko.
A karshe, jaruma Dawayya ta mika godiyarta mai tarin yawa ga masoyanta bisa ga addu’o’i tare da goyon bayansu a gareta.

A lokuta da dama jaruman sukan samu matsala da iyayensu a duk lokacin da suka furta musu cewa suna so su shiga harkar fim, musamman jarumai mata da ake ganin suna da rauni wajen mu’amala da maza.

A kwanakin baya ita ma jaruma Hafsat Idris tayi magana makamanciyar wannan inda take cewa ita ma sai da ta samu matsala da iyayenta da farko kafin su bata damar shiga masana’antar ta Kannywood.

Iyayen suna hana ‘ya’yan nasu shiga harkar ne saboda ganin yadda halayyarsu ke gurbacewa da zarar sun fara fitowa a fim.

NgHausa

I am YusHau Uba, CEO/Founder Of HausaMini.Com.Ng
Back to top button